Majalisar Dokokin Kasar Sudan Ta Kudu Ta Amince Da Yerjejeniyar Sulhu Da Yan Tawayen Kasar

Majalisar Dokokin Kasar Sudan Ta Kudu Ta Amince Da Yerjejeniyar Sulhu Da Yan Tawayen Kasar

A jiya Alhamis ce majalisar dokokin kasar Sudan ta Kudu ta amince da yarjejeniyar sulhu wacce gwamnatin kasar ta cimma da yan tawaye kimanin wata guda da ya gabata.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya nakalto majiyar ma'aikatar shari'a ta Sudan ta kudu tana cewa dalilin jinkiri wajen amincewar majalisar dokokin kasar da wannan yerjejeniyar shi ne, rashin isar yerjejeniyar gaban Majalisar dokokin cikin lokci daga kungiyar EGAD ta raya tattalin arzikin kasashen tsakiyar Afrika.

A cikin watan Satumban da ya gabata ne shugaban kasar Sudan ta Kudu Silva Kiir tare da shugaban kungiyar yan tawaye mafi girma a kasar kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar, suka rattaba hannun kan yerjejeniyar sulhu da kuma raba iko a tsakaninsu.

A bisa wannan yerjejeniyar dai Riek Machar zai koma kan kujerarsa ta mataimakin shugaban kasa na farko, sannan zasu raba sauran mukaman gwamnati a tsakaninsu.

An fara yakin basasa a kasar Sudan ta Kudu ne a cikin watan Decemban shekara ta 2013 shekaru biyu kacal da ballewar kasar daga kasar Sudan.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky