Mahukuntan Masar Sun Zargi Wasu Mutane 28 Da Kokarin Kifar Da Gwamnatin Kasar

Mahukuntan Masar Sun Zargi Wasu Mutane 28 Da Kokarin Kifar Da Gwamnatin Kasar

Babban lauyan gwamnatin Masar mai shigar da kara ya bada labarin cewa: An zargin wasu mutane 28 da hannu a kokarin kifar da gwamnatin kasar.

Nabil Sadiq babban lauyar gwamnatin Masar mai shigar da kara ya sanar da cewa: A halin yanzu haka ana tsare da mutane 9 daga cikin wadanda ake zargi da laifin kafa kungiyar mai suna "Masar domin Samar da Canji" ba a kan doka ba.

Nabil Sadiq ya kara da cewa: Kafa kungiyar ya saba wa kundin tsarin mulkin Masar, kuma ya sabawa doka tare da yin hannun riga da batun hadin kan kasa musamman sakamakon matakin da kungiyar ke dauka na watsa labarun karya a ciki da wajen  kasar da nufin tada hankali da rusa masalahar kasa da kuma janyo cikas a harkokin tattalin arzikin Masar.

Tun bayan sake zabar shugaba Abdul-Fatah Al-Sisi a matsayin shugaban kasar Masar a wa'adi na biyu gwamnatin Masar ta taso 'yan adawa gaba da nufin rufe bakinsu kan barin sukar siyasar gwamnatin kasar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky