Libiya Ta Bukaci Kasar Rasha Ta Dawo Da Ayyukan Ofishin Jakadancinta A Kasar

Libiya Ta Bukaci Kasar Rasha Ta Dawo Da Ayyukan Ofishin Jakadancinta A Kasar

Gwamnatin Libiya ta bukaci ma'aikatar harkokin wajen Rasha da ta dawo da ayyukan ofishin jakadancin kasarta da ke birnin Tripoli fadar mulkin kasar Libiya.

Mataimakin ministan sadarwa a gwamnatin hadin kan kasar Libiya Hisham Abu-Shak'wiwat ya jaddada wajabcin karfafa alakar diflomasiyya tsakanin kasashen Libiya da Rasha tare da jinjinawa kasar ta Rasha kan rawar da take takawa a fagen wanzar da zaman lafiya da sulhu, don haka ya bukaci ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha da ta dawo da ayyukan ofishin jakadancinta da ke birnin Tripoli fadar mulkin kasar ta Libiya.

Hisham Abu-Shak'wiwat ya kara da cewa: A halin yanzu haka da dama daga cikin kasashen yammacin Turai sun bude ofisoshin jakadancinsu da suke birnin Tripoli kuma suna ci gaba da gudanar da ayyukansu, don haka akwai bukatar Rasha ta dauki matakin sake bude ofishin jakadancinta a kasar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

mourning-of-imam-hussain
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky