Libiya: Kasashen Duniya Sunyi Allah Wadai Da Rikicin Libiya

Libiya: Kasashen Duniya Sunyi Allah Wadai Da Rikicin Libiya

Kasashen Amurka Faransa da kuma Italiya da Birtaniya sun yi tir da rikicin baya-bayan nan da ya barke a Tripoli babban birnin Libya da ya kai ga rasa dimbin rayuka, inda suka bukaci bangarori biyu da ke iko da kasar su dau matakin magance sake faruwarsa.

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da kasashen hudu wadda ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta fitar ta ce barkewar makamantan rikicin barazana ce ga shirin zaben kasar dama yunkurin dawo da zaman lafiyar da ake yi.Barkewar sabon rikicin a Tripoli daga ranar Alhamis zuwa daren Juma’a ya hallaka akalla mutane 40 yayinda aka rika ganin makaman roka na keta sararin samaniya matakin da ya tilasta kulle filin jirgin saman kasar guda daya tilo da ke aiki tun bayan yakin basasar 2011.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky