Kenya: An Kashe Wasu Masu Zanga-Zangar Kin Amincewa Da Sakamon Zabe

Kenya: An Kashe Wasu Masu Zanga-Zangar Kin Amincewa Da Sakamon Zabe

Rahotanni daga kasar Kenya na cewa, akalla mutane biyu ne daga cikin masu zanga-zangar kin amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa aka tabbatar da mutuwarsu, sakamakon wata taho mu gama da jami'an tsaro.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, masu zanga-zangar biyu sun mutu ne sakamakon harbi da bindiga da 'yan sanda suka yi a kan masu zanga-zangar a yau Laraba a garin Safi.

Wani jami'in 'yan sanda ya sheda wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa barayi ne suka shiga cikin masu zanga-zangar domin wawushe kayan jama'a, a kan haka suka yi amfani da karfi domin tarwatsa su.

Madugun adawa na kasar Kenya Reila Odinga ya yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a  jiya a kasar, inda ya zargi Uruhu Kenyatta da hukumar zaben kasar da tafka magudi.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky