Karuwar Fataucin Mutane Na Ci Gaba A Libiya

 Karuwar Fataucin Mutane Na Ci Gaba A Libiya

Majalisar Dinkin Duniya ce ta sanar da cewa ana samun kararuwar fataucin mutane a kasar Libya

Kamfanin dillancin labarun Faransa ne ya ambato wasu rahoton sirrin na binciken da kwararrun Majalisar Dinkin Duniya suka gudanar akan kasar libya, wanda kuma aka gabatar wa da mambobi 15 na kwamitin tsaro, wanda a ciki aka yi ishara da karuwar fataucin mutane.

Rahoton mai shafuka 157 ya kuma bayyana yadda take hakkin bil'adama yake karuwa a cikin Libya.

Har ila yau an ambaci yadda kungiyar Da'esh take kokarin kafa alaka da masu fatauncin mutane ta hanyar amfani da kudi.

Rashin tabbas ta fuskar tsaro a kasar Libya ya share fagen bullar fatauncin mutane da kuma sayar da bakaken fata a matsayin bayi.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky