Ivory Coast : Gwamnati Ta Sanar Da Cimma Yarjejeniya Da Sojoji Masu Bore

Ivory Coast : Gwamnati Ta Sanar Da Cimma Yarjejeniya Da Sojoji Masu Bore

Gwamnatin Ivory Coast ta sanar da cimma wata yarjejeniya da sojoji masu bore, saidai ba tare da yin karin haske ba.

Ministan tsaro kasar ne Alain-Richard Donwahi, ya sanar da hakan a gidan talabijin din kasar, wanda ya ce bayan tattaunawa da sojojin sun cimma mastaya ta lalubo yanyoyin kawo karshen boren, ya kuma yi kira ga sojojin da su koma barikinsu. 

Saidai wata majiya daga sojojin masu bore ta shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa babu wata matsaya da suka cimma da gwamnatin, don kuwa babu wani wakilinsu na Buake da ya halarci tattaunawar, iya abunda suka sani taro ne na mayan hafsoshi.

A ranar Asabar ce sojojin suka fantsama kan tituna suna masu bore kan jinkirin da aka samu wajen biyansu kudaden alawas da gwamnati ta yi musu alkawari, bayan sunyi irin wannan boren a watan Janairu aka kuma basu rabin kudaden, sannan a dinga biyansu sauren da kadan- kadan daga bakin watan Mayu.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky