Hukumar NJC A Nijeriya Ta Bukaci A Kori wasu Alkalai

Hukumar NJC A Nijeriya Ta Bukaci A Kori wasu  Alkalai

Hukumar da ke sanya ido kan lamurran shari'a a Nijeriya (NJC) ta bukaci da a sallami wasu alkalai guda biyu a kasar kamar yadda kuma ta ja kunnen sauran alkalan kuma kan ayyukan da suke yi.

Hukumar NJC din ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar a yau din nan inda ta nuna damuwa dangane da ayyukan wasu alakan da kuma jan kunnen wasu ma da su taka tsantsan.

Alkalai biyun dai da hukumar ta bukaci a kora su ne  mai sharia Theresa Uzokwe, babbar mai shari'a ta jihar  Abia da kuma mai sharia Obisike Oji na babban kotun jihar Abia dai. Tana mai cewa ta bukaci a kori mai shari'a  Uzokwe din ne biyo bayan shawarar da wasu kwamitocin bincike suka gabatar bayan sun gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake mata.

Har ila yau kuma sanarwar ta ja kunnen wasu  alkalan da suka hada da S. E Aladetoyinbo da  Olusola Ajibike Williams na babban kotun Abuja da kuma na Lagos, saboda wasu ayyuka da suke yi da hukumar ta ce ba za ta taba amincewa da su ba.

Daya daga cikin zarge-zargen da ake zargin alkalai a Nijeriya din dai shi ne batun rashawa da cin hanci da karbar kudi don murguda shari'a.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky