Harkar Musulunci a Nijeriya ta bugaci Ministan Yada Labaran Nijeriya da ya fito yayi wa duniya bayanin yanda aka yi Sheikh Ibra

Harkar Musulunci a Nijeriya ta bugaci Ministan Yada Labaran Nijeriya da ya fito yayi wa duniya bayanin  yanda aka yi Sheikh Ibra

Harkar Musulunci a Nijeriya ta bugaci Ministan Yada Labaran Nijeriya da ya fito yayi wa duniya bayanin yanda aka yi Sheikh Ibrahim Zakzaky ya zama barazana ga tsaron Kasa.

A wata takarda ta manema labarai da shugaban kungiyar yada labarai na Harkar Musulunci a Nijeriya,Ibrahim Musa ya fitar jiya Juma’a,6 ga watan Oktoba,ya bayyana cewa zamu so Ministan Yada labaran Nijeriya ya fito ya yiwa duniya bayani dalla dalla ta yanda aka yi gwamnatin Buhari ta fahimta akan cewa Sheikh Zakzaky barazana ne ga tsaron Nijeriya.
Mallam Ibrahim Musa a lokacin da yake martani ga Ministan Yada Labaran Nijeriya dangane da  wata hira da yayi da  gidan rediyo na BBC hausa a makon da ya gabata,in da ministan ya bayyana cewa gwamnatin tarayya tana cigaba da tsare Sheikh Zakzaky ne duk da umurnin kotu akan a sake shi saboda wasu dalilai na tsaro.
Sannan ministan ya kara da cewa dalilai da abubuwan da suka shafi  tsaro suna sama da duk wasu hakkoki na mutane wanda tsarin ya tanada ga ‘yan kasa.Sannan yayi kokari ya wanke Shugaban Kasa Muhammadu Buhari in da yayi kokari ya nuna cewa babu hannun Buhari wajen cigaba da tsare Sheikh Zakzaky,da dalilin cewa shi Shugaba Buhari baya shishshigi a cikin lamurran  masu tsaro.
Mallam Ibrahim Musa a cikin martaninsa  ga Lai Muhammad,ya bayyana cewa:
“Fiye da shekara daya  bayan ta’addancin da aka yi wa Sheikh Ibrahim Zakzaky da harkar sa,matsayar gwamnati shine cewa suna rike da Sheikh Zakzaky ne saboda su bashi kariya ta musamman,sannan kuma sun fadawa kotu cewa suna rike da shi(Sheikh Zakzaky) ne ba wai don  ya aikata wani laifi bane.
  “A akan wannan matsayar (ta gwamnati) ne kotu ta yi hukunci da cewa ba a san wani abu wai kariya ta musamman ba a dokokin kasa ba,shi yasa tayi umurni da a gaggauta sakin Sheikh Zakzaky,sannan a biya shi diyya.”
Ibrahim Musa ya kara da cewa da gwamnati ta ga ta fadi kuma bata shirya bin umurnin kotu ba sai ta din ga kame kame jiya tace ai tana so ta gina ma Sheikh Zakzaky gida ne,yau kuma tace ai dalilai da wasu muhimman lamurra na tsaro ne suka sanya ba ta  sake shi ba.
A karshe Ibrahim Musa ya jaddada matsayarsu wanda suka kasance akanta na cewa gwamnati ta gaggauta sakin Sheikh Ibrahim Zakzaky da duk sauran membobinsu wa’yanda ake tsare dasu a wurare daban daban na kasar nan  ba tare da wani sharadi ba.Sannan  ya bayyana cewa suna da hakki su nemi hakkokinsu na ‘yancin yin addini da kuma hakkokinsu na ‘yan kasa..288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

mourning-of-imam-hussain
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky