Harin masallacin Benghazi ya jikkata kusan mutane 100

Harin masallacin Benghazi ya jikkata kusan mutane 100

Wasu hare-haren Bom da tsakar ranar yau a masallacin juma'a da ke birnin Benghazi na Libya ya hallaka mutum guda, yayinda ya jikkata kusan mutane 100.Rahotanni sun ce harin shi ne irinsa na farko a baya-bayan nan da aka kai wurin ibada

Jami’an tsaro sun ce bom na farko an boye shi ne cikin masallacin yayinda na biyu kuma a waje ajiye takalma.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin harin, amma sai dai ya jefa garin cikin rudani.

Ko a ranar 24 ga watan Junairu ma an kai makamancin wannan hari a kan masallatan tare da hallaka kusan mutane 50.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky