Gwamnatin Nigeria Ta Ki Amincewa Da Sharuddan Amurka Na Sayar Mata Da Jiragen Yaki

Gwamnatin Nigeria Ta Ki Amincewa Da Sharuddan Amurka Na Sayar Mata Da Jiragen Yaki

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ki amincewa da sharuddan da gwamnatin Amurka ta shimfida mata don sayar mata da jiragen yaki samfurin A-29 Super Tucano guda 12.

Jaridar Daily Trust ta Nigeria ta nakalto ministan tsaron kasar Mohammed Dan-Ali yana fadar haka ga yan jarida a fadar shugaban kasa, ya kuma kara da cewa sharuddan sun hada da cewa, ba za'a sayarwa Nigeria jiragen ba sai shekara ta 2020, sannan Amurka ba  zata horar da yan Nigeria sanin yadda jiragen suke aiki ba ko kuma yadda zasu kula da su ba.  Banda haka akwai batun cewa Amurka ba zata bar injiniyoyin Nigeria su kasance a wuraren da ake harhada jiragen kamar yadda aka saba a wasu kasashe ba. 

Ministan ya ce, a lokacin da suka sayi jirage masu saukar Ungulu samfurinn  ML35 daga kasar Rasha, injiniyoyin Nigeria sun kasance tare da ma'aikatan kamfanin kera jiragen har aka kammala. Kuma haka yake a duk lokacin da suka kulla irin wannan yerjejeniyar da sauran kasashen duniya. 

Banda haka ministan ya ce gwamnatin Amurka ta yi ta daga batun tattaunawa cinikin jiragen kan batutuwan kare hakkin bil'adama a kasar tun lokacin shugabancin Barack Obama.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky