Gwamnatin Mali ta dage zaben kananan hukumomi

Gwamnatin Mali ta dage zaben kananan hukumomi

Gwamnatin kasar Mali ta sanar da jinkirta zabukan kananan hukumomi, saboda matsalar rashin kwanciyar hankali, sakamakon tashin hankalin da ake samu a sassan kasar.

Aboubacar Sidick Fomba, shugaban hukumar zaben, yace an dage zaben kananan hukumomin daga watan Disamba zuwa Afrilu na shekara mai zuwa.

Tashe tashen hankulan da ake samu sun yi sanadiyar hallaka sojojin Majalisar Dinkin Duniya 4 da na Mali guda da kuma jikkata wasu 21.

A ranar Asabar da ta gabata, hukumomin tsaron Mali suka tabbatar da mutuwar dakarun wanzar da zaman lafiyar 4 sakamakon harin da ‘yan tawaye suka musu a yankin Menaka da ke arewa maso gabashin kasar.

Sai dai rundunar ta MINUSMA ta ce dakarunta sun hallaka mayakan ‘yan tawayen da dama, a martanin da suka mai da.

A ranar 26 ga watan Oktoban da ya gabata, sai da ‘yan tawayen na Mali suka hallaka wasu dakarun rundunar ta MINUSMA 4, da suka fito daga Chadi, bayan da motar su ta taka nakiyar da aka dasa musu

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky