DRC : 'Yan Sanda Sun Yi Harbi Kan 'Yan Katolika Dake Zanga-zangar Kin Jinin Gwamnati

DRC : 'Yan Sanda Sun Yi Harbi Kan 'Yan Katolika Dake Zanga-zangar Kin Jinin Gwamnati

Rahotanni daga Jamhuriya Demukuraddiyar Congo na cewa mutane biyu suka raunana sakamakon harbi da bindiga da 'yan sanda suka yi kan 'yan Katolika dake zanga -zangar kin jinin gwamnati.

Tunda farko dai 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye don tarwatsa masu zanga-zangar da suka fito daga coci, kafin daga bisani su fara harbi da harsashen bindiga.

Bayanai daga kasar sun ce an cafke wasu maluman Coci uku. 

Gungun kungiyoyin na 'yan Katolika (CLC) a wannan kasa na neman shugaban kasar Joseph Kabila, da ya bayyana cewa ba zai tsaya takara ba a zaben shugabancin kasar na 23 ga watan Disamba 2018


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky