Dino Melaye Ya Tsallake Rijiya Ta Baya

Dino Melaye Ya  Tsallake Rijiya Ta Baya

Yunkurin yi wa dan majalisar dattijan Najeriya mai wakiltar yammacin jihar Kogi Dino Melaye ya kiranye yaci tura

Sakamakon kuri’ar da hukumar zaben Najeriya INEC ta jihar Kogi ta wallafa ya nuna cewa kashi 5.34% ne kawai na masu neman yiwa dan majalisar kiranye suka bayyana, a maimakon akalla kashi 50% da doriya da kundin tsarin mulkin Najeriya ya fayyace.

A kunshe cikin sakamakon zaben da hukumar INEC ta fitar, yankin yammacin Kogi yana da yawan masu kada kuri’a da suka kai 351,140.

Hukumar ta ce daga cikinsu masu kada kuri’ar, kusan mutane daga mazabar dan majalisar 190,000 ne suka sa hannu kan amincewa da kiranyen amma ajiya Asabar mutane 20, 868 ne kawai suka bayyana domin a tantance su, dan haka hukumar bata da ikon kai ga mataki na gaba wajen aiwatar da kada kuri’an yiwa dan majalisar dattijan kiranye.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky