Ci Gaba Da Kisan Jama'a A Zamfara Na Tada Hankalin Gwamnatin Najeriya

Ci Gaba Da Kisan Jama'a A Zamfara Na Tada Hankalin Gwamnatin Najeriya

Bisa dukkan alamu ci gaba da kisan bayin Allah a jihar Zamfara na Nigeria ya tasar da hankulan mahukuntan Najeriya da tilasta masu maida hankula jihar a yanzu haka.

Ministan Tsaro Mansur Dan Ali wanda dan asalin jihar ce ya koma jihar domin ganin an dauki matakan magance lamarin.

Shima Babban Sufeto Janar na 'Yan Sandan kasar Ibrahim Idris na jihar Zamfara tare da ayarin manyan 'yan sanda domin tattauna irin matakan da suka dace a dauka.

Ibrahim Idris har ya ziyarci Sarkin  Zurmi Alhaji Abubakar Atiku Mohammed inda yake  cewa yawan kisa da ake samu a Zamfara na neman wuce gona da iri.

Tsakiyar makon daya gabata ne wasu 'yan bindiga suka kashe mutane 40 a kauyen Birane dake karamar hukumar Zurmi.

ÀWannan shine na baya-bayan nan kisa da ake samu akai-akai a jihar.

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky