Barayin Shanu sun hallaka mutane 30 a Zamfara

Barayin Shanu sun hallaka mutane 30 a Zamfara

Barayin shanu sun hallaka akalla mutane 30 a wasu jerin hare-hare da suka kai kan wasu kauyukan jihar Zamfara da ke karamar hukumar Maradun a yammacin ranar Talata.

Wani shugaban al’umma a kauyen Gyadde Jabbi Labbo ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, barayin shanun sun kai samamen bisa Babura inda suka yi awon gaba da tarin dabbobi, da suka hada da Shanu, tumaki da awaki.

Labbo ya ce kauyukan da aka kaiwa harin sun hada da Sakkida, Farin Zare, Orawa, Gyadde da kuma Sabon Gari.

Sai dai yayin tabbatatr da cewa an kai hare-haren, rundunar ‘yan sandan jihar ta Zamfara ta ce mutane 3 kawai barayin shanun suka hallaka, kamar yadda kamfanin dillancin labaran AFP ya rawaito.

A makon da ya gabata ne, wasu ‘yan bindiga haye kan Babura suka hallaka, akalla mutane 32, a wasu kauyukan da ke kan iyakar jihohin Zamfara da Sokoto.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky