Azhar: Wajibi Ne A Shiga Kafar wando Daya Da Masu Yada Tsatsauran Ra'ayi

Azhar: Wajibi Ne A Shiga Kafar wando Daya Da Masu Yada Tsatsauran Ra'ayi

Babban malamin Azahar Ahamd Tayyib ya sanar da kafa kwamiti, domin bin diddigin fatawowyin da malamai da ake fitarwa a kasar Masar, da nufin hana fitar da fatawoyi da ke yada tsatsauran ra'ayi.

Kamfanin dillancin labaran INA ya bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da lauya mai kula harkokin shari'ana cibiyar Azahar Muhammad Abdulsalam ya fitar, ya bayyana cewa Sheikh Ahmad Tayyib ya kafa wannan kwamiti ne da nufin ganin an kawo karshen fatawowin tunzura jama'a da kafirta musulmi, wanda hakan ke haifar da ayyukan ta'addanci.

Ya ce yanzu haka kwamitin wanda ya hada da malamai da kuma masana kan harkokin shari'a ya fara gudanar da aikinsa, ta hanyar tuntubar manyan malamai da kuma sanin abubuwan da suke wakana a dukkanin cibiyoyin addini.

A cikin wani bayani da cibiyar ta Azhar fitar a kwanakin baya ta bayyana cewa, masu akidar kafirta musulmi dai sun taka gagarumar rawa wajen wanke kwakwalen wasu matasa a kasar, wanda hakan ya sa suka shiga kungiyoyin ta'addanci tare da kai hare-haren bama-bamai a cikin kasar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky