Ana Harbe-harben Bindigogi A Cikin Biranan Abijan Da Boake Na Kasar Ivory Coast

Ana Harbe-harben Bindigogi A Cikin Biranan Abijan Da Boake Na Kasar Ivory Coast

Sojojin da suke yin bore a kasar Ivory Coast na yin harbe-harben bindigogi a cikin biranan Abijan da Bouake.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, tun da jijjifin safiyar yau ake jin karar harbe-harben bindigogi a cikin yankin Ekuido da ke gabashin birnin Abijan cibiyar kasuwancin Ivory Coast, lamarin da yasa aka killace jama'a tare da hana su isa yankunan gabashin birnin a yau.

A can birnin Bouake ma a yau an ji harbe-harben bindiga a sassa daan-daban na birnin, yayin da sojoji a cikin motoci masu sulke suke ta sintiri a kan manyan titunan birnin.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky