An yiwa Tsarin Zaben Najeriya Garambawul

An  yiwa Tsarin Zaben Najeriya Garambawul

Majalisar Wakilai ta Najeriya ta yi gyara a dokar zabe wanda ya nuna yanzu za a fara zaben ne da na majalisa kafin zaben shugaban kasa.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta tsara yadda za a gudanar da zaben shekara ta dubu biyu da goma sha tara, inda ta tsara cewa za a fara zaben da na shugaban kasa da kuma na ‘yan majalisun dokokin tarayya, amma a sabuwar dokar, ‘yan majalisar sun maida zaben shugaban kasa baya.

Da yake tsokaci dangane da batun, Ahmed Babba Kaita dan jam’iyar APC a majalisar wakilai ya bayyana cewa, akwai rauni a sabon tsarin domin bai kamata a raba zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasa amma a kyale a gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar dokokin jiha a rana daya.

Bisa ga cewarshi, an nemi yin wannan gyaran ne da wata manufa ta dabam, a nashi ra’ayin masu neman a gudanar da wannan tsarin mutane ne da basu yiwa al’ummarsu komai ba sabili da haka suna fargaban tsayawa takara kada su fadi zabe, shine suke kokari yiwa jam’iyar APC illa.

Shi kuwa a nashi tsokaci, Timothy Ngolu Simon na jam’iyar PDP, yace su da suka goyi bayan gyaran dokar a majalisa basu yi shi da wani nufi ba, Yace an maida tsarin dokar ne yadda take tun farko. Yace da wannan tsarin aka gudanar da zaben da ya sa tsohon shugaba Olusegun Obasanjo ya hau mulki kafin daga baya ya sauya shi. Bisa ga dukan alamu ‘yan jam’iyar APC basu goyon bayan wannan sabon tsarin.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky