Wata kotu a birnin Eskandariya na kasar Masar ta yanke hukuncin kisa kan mutane 17 wadanda ta tabbatar da laifin kai hari kan coci-coci da kuma kashe kiristoci a wurare daban daban a cikin kasar.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto shafin yanar gizo na labarai mai suna "Ahl-Misr" yana fadar haka a shafinsa a yau Alhamis, ya kuma kara da cewa banda mutane 17 wadanda ta yankewa hukunci kisa, Kotun ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai kan mutane 19, sannan daurin shekaru 15 kan wasu mutane 9, sai kuma mutun guda daurin shekaru 10 a gidan kaso.
Laifuffukan da tabbatawa mutanen dai sun hada da kisan kiristoci 82 a cikin cocin Al-Badrisiyya a unguwar Abbasiya na birnin Alkahira, da kuma Cocin "Mori Jojis" a birnin Tantaa da kuma kai hari kan Cocin Al-markisiyya na birnin Eskandariya.
Banda haka wasu daga cikin nwadanda aka yenkewa hukuncin a yau alhamis sun kashe yansanda 8 ta hanyar sanya tada bom a cikin wani coci da kuma barin wuta kan kiristoci Kibtawa a birnin Eskandariya.
Labarin ya kara da cewa dukkan wadannan laifuffukan an aikatasu ne a tsakanin shekara 2011-2017.