An Yanke Hukuncin Kisa Kan Mutum 6 A Masar

An Yanke Hukuncin Kisa Kan Mutum 6 A Masar

Kotun hukunta manyan laifuka ta birnin Alkahira ta yanke hukuncin kisa wasu mutum 6 a jiya Talata.

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya habarta cewa a jiya talata kotun hukunta manyan laifuka ta birnin Alkahirar Masar ta yanke hukuncin kisa kan wasu mutum 6 bisa laifin kai hari a kan wani wurin bincike na jami'an tsaro a arewacin birnin a shekarar 2016.

Har ila yau kotun ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga wasu mutum biyu, sannan kuma ta yanke hukuncin dauri ga wasu mutum 4 na daban daga shekaru 3 zuwa 15 a gidan Kaso.

Rahoton ya ce yayin da aka kai hari an hallaka wani jami'in dan sanda.

Bayan laifin kai harin a wurin binciken 'yan sanda, kotun na zarkin wadannan mutane da kafa kungiyar ta'addanci a kasar

A cikin watanin baya-bayan nan gwamnatin kasar Masar na zartar da matakai da dama na kalubalantar kungiyoyin 'yan ta'adda.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky