An Tarwatsa Wani Sansanin 'Yan Ta'adda A Kan Iyakokin Kasashen Nijar Da Burkina Faso

An Tarwatsa Wani Sansanin 'Yan Ta'adda A Kan Iyakokin Kasashen Nijar Da Burkina Faso

Rahotanni daga kasar Nijar sun bayyana cewar sojojin kasar sun sami nasarar tarwatsa wasu sansanonin kungiyoyin 'yan ta'adda da ke kan iyakokin kasar da kasar Burkina Faso.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya ba da rahoton cewa a wata sanarwar da Ma'aikatar cikin gidan kasar Nijar din ta fitar, ta ce a yayin wasu hare-haren da sojojin kasar  suka  kai wasu yankuna na Kudu maso yammacin kasar, sun sami nasarar tarwatsa wasu sansanonin 'yan ta'adda da suke kan iyakar kasar da kasar Burkina Faso.

Sanarwar ta kara da cewa har ila yau rundunar sojin ta Nijar ta jibge wasu jami'an sojinta a wadannan yankuna don ci gaba da tsarkake shi daga 'yan ta'addan da suka dauki wajen a  matsayin wata tungarsu.

Tun a watannin da suka gabata ne dai gwamnatin Nijar din ta tsara da kuma fara aiwatar da  wani shiri na fada da 'yan ta'addan a yankin Torodi da ke kudu maso yammacin kasar don kawo karshen 'yan ta'adda da suke ci gaba da gudanar da ayyukansu a kasar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky