An kame wanda ake zargin da satar turawa a Kaduna

An kame wanda  ake zargin da satar turawa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi nasarar kame mutumin da ake zargin shi ne shugaban gungunar masu satar mutanen da suka yi garkuwa da turawan nan hudu na Amurka da Canada, cikin makon da ya gabata, yayin da suke kan hanyar komawa Abuja daga Kafanchan, inda suka je aiki.

An kame mutumin dake da sunan Dogo Russia ne a yankin karamar hukumar Kagarko da ke Kaduna, inda aka kwace bindigogi kirar AK 47 daga hannunsa.

Wanda ake zargin ya kuma amsa cewar tabbas sune suka hallaka ‘yan sandan da ke bai wa turawan tsaro a lokacin da suka dace su, a ranar talatar makon da ya gabata.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky