An Hallaka Wani Komandan Kungiyar Ashabab A Somaliya

An Hallaka Wani Komandan Kungiyar Ashabab A Somaliya

Ma'aikatar sadarwa ta kasar Somaliya ta sanar da hallaka wani komandan kungiyar ta'addanci ta Ashabab.

Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto ma'aikatar sadarwa ta kasar somaliya na cewa sojojin kasar sun samu nasarar hallaka Ali Mohamad Husaini wanda aka fi sani da Ali Jabal, shi dai  wannan mutum na daga cikin manyan komondojin da kungiyar Ashabab ke ji da su, kuma shi ne ya shirya hare-haren ta'addancin da aka kaiwa jami'an tsaron kasar a yankin Torturou dake kudancin kasar.

Wannan hari da Sojojin Somaliyan suka kaiwa mayakan Ashabab, shi ne irinsa na biyu cikin watanni biyu na bayan bayan nan da yayi sanadiyar hallaka mayakan na Ashabab da dama.

Idan ba a manta ba tun a watan Augustan shekarar 2011 ne Dakarun tsaron Somaliya tare da hadin gwiwar dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar kasashen Afirka Amison suka samu nasarar fatattakar mayakan Ashabab din daga magadushu babban birnin kasar.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky