An hallaka Fulani Makiyaya dubu guda -Miyetti Allah

An hallaka Fulani Makiyaya dubu guda -Miyetti Allah

Hadakar kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta yi ikirarin kisan fiye da mambobinta makiyaya dubu guda sakamakon rikice-rikicen da su ke fuskanta tsakaninsu da manoma a sassan Najeriya.

A cewar kungiyar cikin wata sanarwa da ta fitar bayan kammala taron manema Labarai iyakar kashe-kashen da suka iya tattarawa alkaluma sun nuna an kashe musu mambobi dubu guda yayin da aka hallaka musu shanu fiye da milyan biyu yayin rikicin da ya faru a jihohin Benue da Taraba dama wasu sassan kasar.

Sanarwar dauke da sa hannun babban sakataren kungiyar na kasa Baba Othman-Ngelzarma ta kuma kalubalanci ikirarin da gwamnatin Benue ta yi na cewa Fulanin ne suka hallaka fiye da mutane 80 da ta yiwa jana’izar bai daya cikin makon jiya.

Sanarwar ta bayyana cewa kungiyar Miyetti Allah ba ta da fatan da ya wuce ganin an kawo karshen makamantan rikice-rikicen don ganin kowa ya zauna lafiya.

Ko a tsakaddaren jiya ma wasu ‘yan bindiga da aka bayyana da Fulani Makiyaya sun kai sabbin hare-hare wasu kauyuka da ke birnin Gwari a jihar Kaduna da ke arewacin kasar tare da hallaka mutane da dama baya ga kone gonaki


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky