An Gudanar Da Gagarumar Zanga-Zangar Neman Sakin Sheikh El-Zakzaky A Najeriya

An Gudanar Da Gagarumar Zanga-Zangar Neman Sakin Sheikh El-Zakzaky A Najeriya

Al'ummar musulmi mabiya mazhabar Shi'a almajiran sheikh Ibrahim Elzakzaky na ci gaba da gudanar da zanga -zanga neman a saki jagoran nasu.

Rahotanni daga Nijeriya sun bayyana cewa a jiya Laraba duban al'ummar musulmi mabiyar mazhabar shi'a  ne suka gudanar da zanga-zanga a biranan  kasar daban daban ciki kuwa har da  Abuja babban birnin kasar, inda suka bukaci gwamnatin tarayya da ta bi umarnin kotu ta kuma saki sheikh Zakzaky da mai dakinsa.

Mahalarta zanga-zangar sun nuna bacin ransu kan yadda gwamnati ta nuna halin ko in kula a game da kireye-kirayen da al'umma ke yi na neman sakin jagoran nasu shekh Ibrahim Elzakzaky.

A ranar 13 ga watan Dicembar 2015 ne sojojin Najeriya suka kai hari kan husainiya bakiyatullah dake garin Zariya na jahar Kaduna dake shiyar arewacin kasar.

A yayin kai wannan farmakin sojojin Najeriyan sun kashe dariruwan magoya bayan Shekh Elzakzaky cikinsu kuwa har da 'ya'yansa uku, sannan kuma suka yi awan gaba da shi tare da maidakinsa.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky