An Gudanar Da Bikin Rantsar Da Shugaban Kasar Kenya Uhuru Kenyatta A Wa'adin Shugabancinsa Na Biyu

An Gudanar Da Bikin Rantsar Da Shugaban Kasar Kenya Uhuru Kenyatta A Wa'adin Shugabancinsa Na Biyu

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya yi rantsuwar kama aiki a wa'adin shugabancinsa na biyu kuma na karshe a babban filin wasanni na birnin Nairobi fadar mulkin kasar a yau Talata.

Kamfanin dillancin labaran Reuter ya bayyana cewa: Dubban magoya bayan shugaba Uhuru Kenyatta ne suka halacci bikin rantsuwar kama aikinsa a yau Talata a wa'adin shugabancinsa na biyu na tsawon shekaru biyar kuma na karshe kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya shimfida a babban filin wasanni na birnin Nairobi fadar mulkin kasar, inda babbar magatakardar ma'aikatar shari'ar kasar Anne Amadi ta jagoranci gudanar da rantsuwar. 

A gefe guda kuma jami'an tsaron Kenya sun yi amfani da iskar gas mai sanya hawaye domin tarwatsa gungun 'yan adawa da suka yi yunkurin tunkarar wajen gudanar da bikin rantsar da shugaban kasar da nufin kawo cikas kamar yadda suka shelanta a baya.

Daga cikin shugabannin kasashe da suka halacci bikin rantsar da Uhuru Kenyatta a wa'adin shugabancinsa na biyu a yau Talata sun hada da Hailemariam Desalegn na Ethiopa da Paul Kagame na Ruwanda da Muhammad Abdullahi Muhammad na Somaliya da Salva Kirr na Sudan ta Kudu da Ian Khama na Botswana da kuma Yoweri Museveni na kasar Uganda. Kamar yadda shugabannin kasashen yammacin Turai suka wakilta jakadunsu a kasar ta Kenya domin halattar bikin.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky