Alal Akalla Mutane 18 Sun Mutu Sakamakon Wani Harin Kunar Bakin Wake A Jihar Borno

Alal Akalla Mutane 18 Sun Mutu Sakamakon Wani Harin Kunar Bakin Wake A Jihar Borno

Rundunar 'yan sandan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya ta bayyana cewar alal akalla mutane 18 sun rasa rayukansu kana wasu kuma kimanin 22 sun sami raunuka sakamakon wani harin kunar bakin wake da aka kai karamar hukumar Konduga a daren jiya Juma'a.

Yayin da yake sanar da labarin, kwamishinan 'yan sandan jihar Bornon, Damian Chukwu ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da wasu 'yan kunar bakin wake da ake tsammanin 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai hari kauyen Kasuwan Kifi, da ke karamar hukumar Kondugan da ke kimanin kilomita 25 daga garin Maiduguri, babban birnin jihar Bornon.

Maharan dai sun kai harin ne kasuwar Kauyen Kasuwan Kifi da take ci da dare inda mutane suke sai da kifi da sauran kayayyakin abinci, inda wanda ya kai harin ya tada bama-baman da ke jikinsa a tsakaniyar jama'a da misalin karfe 8 da daren jiyan.

A baya-bayan nan dai 'yan kungiyar Boko Haram din sun koma kai hare-haren kunar bakin wake cikin jama'a sakamakon ci gaba da takura musu da sojojin Nijeriya suke yi wanda ya zuwa yanzu sun karya lagon kungiyar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky