Al Bashir na Sudan zai kauracewa taron Saudiya da Trump zai halarta

Al Bashir na Sudan zai kauracewa taron Saudiya da Trump zai halarta

Shugaban Sudan Omar Hassan al Bashir da kotun duniya ta ICC ke tuhuma da aikata laifukan yaki, ya sanar da kauracewa taron shugabannin kasashen Musulmi da za a gudanar a Saudiya tare da shugaban Amurka Donald Trump.

Kamfanin dillacin labaran Sudan ya ruwaito wata sanarwa daga fadar shugaban kasar da ke bayyana neman afuwar Sarki Salman na Saudiya kan kauracewar al Bashir a taron da za a gudanar ranar Lahadi a Riyadh.

Sanarwar ta ce al Bashir zai kauracewa taron ne saboda wasu dalilai na kashin kansa.

Kotun ICC ta dade tana farautar shugaban na Sudan kan zargin aikata laifukan yaki a rikicin Darfur inda dubban mutane suka mutu.

Shugaban Amurka Donald Trump zai halarci taron tare da gabatar da jawabi kan fatar zaman lafiya.

Saudiya dai ba ta cikin mambobin kasashen da suka amince da kotun ICC, amma ofishin jekadancin Amurka a Khartoum ya yi gargadin kaucewa gayyatar shugaba al Bashir da kotun ta bada sammacin kama shi.

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky