Akwai Yiyuwar Zuwa Zagaye Na Biyu A Zaben Shugaban Kasar Saliyo

Akwai Yiyuwar Zuwa Zagaye Na Biyu A Zaben Shugaban Kasar Saliyo

Hukumar zaben Saliyo ta sanar da sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar Laraba da ta gabata

A jiya asabar ne hukumar zaben kasar ta fitar da sakamakon farko na zaben shugaban kasar da aka yi ranar larabar da ta gabata, inda dan takarar jam'iyar APC mai milki Mr Kamara  ya samu kuri'a 566, 113, yayin da babban abokin hamayarsa Mr Bio Julius Maada ya samu kuri'a 564, 687.

Shugaban hukumar zaben Mr Mohammed Nfah Conteh ya ba al`uma hakuri saboda jinkirin da hukumarsa ta yi kafin ta sanar da bangaren sakamakon. sannan ya ce wannan shi ne sakamakon kashi 50 cikin dari na kuri`un da aka kidaya, da kuma hukumar zabe ta tantance su.lamarin da al'uma ke ganin cewa akwai yiyuwar zuwa zagaye na biyu.

Kimanin 'yan takara 16 dai suka zagawarcin kujerar shugaban kasar ta Saliyo


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky