Afirta Ta Tsakiya: An Kai Wa Dakarun Zaman Lafiya Hari Da Makamai.

Afirta Ta Tsakiya: An Kai Wa Dakarun Zaman Lafiya Hari Da Makamai.

Kamfanin dillancin labarun Reuters ya ce; Kungiyar "Anti Balaka" mai dauke da makamai ce ta kai wa dakarun tabbatar da zaman lafiya na MDD hari a jiya lahadi.

An kai harin ne a garin  Bangassou mai nisan kilo mita 100 daga babban birnin kasar. Kawo ya zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar sojan Masar da ke cikin rundunar guda daya, da kuma jikkata wasu guda uku.

A cikin wannan shekarar ta 2017 kadai an kashe dakarun zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya 13.

Kasar Afirka ta tsakiya ta fada cikin rikicin siyasa ne a 2013 wanda ya sauya zuwa na addini da kabilanci.

Kungiyar "Anti Balaka" mai dauke da makamai ta kashe musulmin kasar da dama tare kuma da tilasta wa wasu dubbai yin hijira.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky