Majalisar Dinkin Duniya Tana Goyon Bayan Kwace Birnin Idlib Daga Hannun Yan Ta'adda

Majalisar Dinkin Duniya Tana Goyon Bayan Kwace Birnin Idlib Daga Hannun Yan Ta'adda

Babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya bayyana cewa yakar yan ta'adda wadanda suke iko da birnin Idlib na kasar Siriya wajibi ne.

Kamfanin dillancin labaran Fars na kasar Iran ya bayyana cewa babban sakatarin ya fadi haka ne a jiya talata ya kuma kara da cewa ba zai taba yiyuwa a sassautawa yan ta'adda ba. 

Kasashen yamma musamman Amurka suna adawa da hare-haren da gwamnatin kasar Siriya ta fara kaiwa yan ta'adda wadanda suke mamaye da birnin Idlib tungarsu ta karshe a kasar Siriya, har ma suna barazanar farwa kasar Siriya da yaki idan ta yi kokarin kwace birnin, da sunan ta yi amfani da makaman guba a kan fararen hula..


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky