Kungiyar EU Ta Yi Allah Wadai Da Hukuncin Kisa Da Aka Yanke Kan 'Yan Kungiyar Ihwan A Masar

Kungiyar EU Ta Yi Allah Wadai Da Hukuncin Kisa Da Aka Yanke Kan 'Yan Kungiyar Ihwan A Masar

Kungiyar tarayyar Turai ta yi Allah wadai da hukuncin kisa da wata kotu a Masar ta yanke kan 'yan kungiyar Ihwanul-Muslimin magoya bayan hambararren shugaban kasar Mohammad Morsi.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya watsa rahoton cewa: Kungiyar Tarayyar Turai a jiya Talata ta fitar da sanarwar yin Allah wadai da hukuncin da kotun shari'ar manyan laifuka ta birnin Alkahira ta kasar Masar ta yanke kan 'yan kungiyar Ihwanul-Muslimin ta kasar su 75, kungiyar tana mai bayyana shakkunta kan bin matakan adalci wajen gudanar da shari'ar 'yan kungiyar ta Ihwan.

Tun a ranar Asabar da ta gabata ce kotun shari'ar manyan laifuka ta birnin Alkahira ta Masar ta yanke hukuncin kisa kan 'yan kungiyar Ihwanul-Muslimin magoya bayan tsohon hambararren shugaban kasar Muhammad Morsi su 75 kan zargin hannu a tarzomar ranar 14 ga watan Agustan shekara ta 2013 tsakanin sojojin gwamnatin Masar da magoya bayan kungiyar Ihwan da suke taron gangami a dandalin Rabi'atul-Adwiyyah da ke birnin Alkahira kan nuna rashin amincewarsu da juyin mulki da sojoji suka yi wa zababbiyar gwamnatin Muhammad Morsi lamarin da ya janyo hasarar rayukan daruruwan mutane tare da jikkatan wasu daruruwa na daban.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky