Koriya ta Arewa ta jingine shirinta na nukiliy

Koriya ta Arewa ta jingine shirinta na nukiliy

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya sanar da dakatar da duk wasu gwaji da kera makaman nukiliyar da kasar ke yi, ya ce babu mahinmancin ci gaba da shirin a yanzu.

A cikin sanarwar shugaban, ya yaba da nasarorin da kasar ta samu inda ya jinjinawa 'yan kasar da suka jajirce don ganin sun samarwa kasar kariya, sai dai ya ce yanzu haka babu mahinmancin ci gaba da yin gwaje-gwaje,maimakon haka zai mayar da hankali kan bunkasa tattalin arzikin kasa.

Shugaba Kim ya kara da cewa gwamnatin Pyongyang a shirye ta ke ta bayar da na ta taimakon a kokarin kawar da barazanar da ke tattare da makaman nukiliya, ya kuma ce kofa a bude ta ke don shiga zaman tattaunawa da makwabtan kasar dama sauran kasashen duniya.

Tun bayan wannan sanarwar ta ba zata, shugabanin kasashen duniya suka soma mayar da martani, shugaba Donald Trump na Amirka ya baiyana farin cikinsa tare da fatan ganawa da shugaban kasar nan ba da jimawa ba. Shi kuwa Firaiministan Japan Shinzo Abe, ya ce ya na matukar farin ciki da wannan ci gaba amma abinda ke da mahinmanci shi ne a gani a kasa.

Takaddama kan shirin nukiliyar Koriya ta Arewa ta haifar da tsamin dangantaka tsakaninta da kasashen duniya musamman Koriya ta Kudu da Amirka da kuma Japan da lamarin ya fi fusatawa. Wannan na zuwa ne kafin a kai ga ganawar Trump da Kim da aka tsara yi a watan Yulin wannan shekarar don ganin an kawo karshen shirin makamai masu linzami na Koriya ta arewa da ke barazana ga zaman lafiyar duniya.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky