An Nada Sabon Shugaban Hukumar DSS A Nigeria

An Nada Sabon Shugaban Hukumar DSS A Nigeria

Shugaban Muhammadu Buhari a tarayyar Najeriya ya nada sabon shugaban hukumar DSS ta kasa

Jaridar Primiumtimes ta Najariya ta nakalto Malam Garba Shehu mai bawa shugaban kasa shawara kan al-amuran watsa labarai yana fadar haka a jiya Alhamis, ya kuma kara da cewa sabon shugaban hukumar yansandan ciki, shi ne Yusuf Magaji Bichi, kuma zai karbi aikin shugabancin hukumar ne daga hannun Matthew Seiyeifa, wanda yake shugabancin riko tun a hukumar bayan da aka tube Lawan Daura a cikin watan da ya gabata.

Yusud Magaji Bichi dai ya dade yana aiki a hukumomin tsaro na kasar, ya kuma yi karatun sakandari a kolejin Danbatta, sannan Kano State College of Advanced Studies daga nan ya sami digiri na farko a jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria. Banda haka ya sami horo a bangaren ayyukan leken asiri a kasar Britani da kuma cikin gida. Ya kuma rike mukamin shugaban hukumar ta DSS a jihohin igawa, Niger, Sokoto da kuma Abia.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky