Amurka, Da Kawayenta Sun Kai Wa Siriya Hari

Amurka,  Da Kawayenta  Sun Kai Wa Siriya Hari

Kasashen Amurka da Birtaniya da kuma Faransa, sun kai wa kasar Siriya harin soji a cikin daren jiya Juma'a wayewar safiyar wannan Asabar, kan abunda suka kira maida martani a kan shugaba Bashar Al'Asad na Siriya bisa zarginsa da amfani da makami mai guba a yankin Duma dake kusa da birnin Damascos a ranar 7 ga watan nan.

Sakataren tsaron Amurka James Mattis ya ce an kaddamar da hare haren ne kan cibiyoyin bincike na makamai masu guda a kusa da birnin Damascos na Siriya.

A cikin daren na jiya ne dai shugaba Donald Trump na Amurka, ya sanar da shirin kai harin na soji kan kasar ta Siriya, tare da hadin gwiwa Faransa da Birtaniya, wanda a cewarsa na ladabdatar da gwamnatin Bashar Al'asad.

Daga bisani ne shugaban kasar Faransa da kuma Firaministar Birtaniya suka sanar da daukan matakin sojin kasashen nasu kan kasar ta Siriya.

An dai kai harin ne ba tare da sanar da kasar Rasha ba, saidai kafin hakan shugaba Macron na Faransa ya ce an dauki duk matakan da suka dace don kaucewa kai hari kan dakarun Siriya da kuma Iraniyawa dake kasar ta Siriya.

A halin da ake ciki dai Amurka ta sanar da kawo karshen hare-haren da aka kwashe kusan sa'a guda ana kai wa.

Babu dai karin bayyani akan irin barnar da hare haren suka haifar.

Hare-haren dai na zuwa ne a daiida lokacin da wata tawagar kwararu ta hukumar da ke kula da hana bazuwar makamai masu guba (OPCW) ta isa Siriya dan gudanar da bincike a yau Asabar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky