Amurka Ba Ta Da Iko Da Tattalin Arzikin Iran

Amurka Ba Ta Da Iko Da Tattalin Arzikin Iran

Mai Ba Wa Jagoran Juyi Shawara akan harkokin soja, Janar Yahya Safawi ya ce Kasar Amurka wacce ba ta da kyakkyawan tarihi a Iran, ba ta da wani iko akan tattalin arzikin Iran

Sayyid Yahya Safawi wanda yake gabatar da jawabi a yau Asabar ya bayyana cewa; Bayanan da aka fito da su daga ofishin jakadancin Amurka suna nuni da cewa Amurka tana goyon bayan kungiyoyin 'yan ta'adda tun farkon cin nasarar juyin musulunci

Janar Afawi ya kuma ce Kasar ta Amurka ce dai ta goya wa Saddam baya a harin da ya kai wa a Iran.

Safawi ya kara da cewa; Daga 1953 da Amurka ta yi juyin mulki a Iran har zuwa kifar da gwamnatin Sha a 1979 Amurkan ce ta rika iko da Iran, don haka duk wani laifi da aka tafaka da sunanta aka yi.

Bugu da kari Janar Safawi ya ce; Karfin da Amurkan take takama da shi yana raguwa a duniya kuma 'yan gwgawarmaya su ne suke samun karbuwa.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky